Biography here....... to be continued

MATAIMAKIN SHUGABAN KASA OSINBAJO YA TSALLAKE RIJIYA DA BAYA !!!! (OSINBAJO)

0

Jirgi mai saukar ungulu dauke da mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya yi hatsari ranar Asabar.Wani sako da kakakin mataimakin shugaban kasar, Laolu Akande ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce jirgin ya yi hatsari ne a jihar Kogi da ke arewa ta tsakiyar kasar.

“Jirgi mai saukar ungulu na mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya yi saukar gaggawa a Kabba, amma shi da ma’aikatan jirgin suna cikin koshin lafiya. Yana ci gaba da ayyukan da suka kai shi jihar Kogi”.
Ya kara da cewa “Mun gode wa Allah, mai kare kowa da komai da ya kare mu; da kuma matuka jirgin bisa jajircewarsu.”
Da yake jawabi a fadar Obaro na Kabba jim kadan bayan hatsarin jirgin, Farfesa Osinbajo ya gode wa Allah bisa tsallake rijiya da baya.
“Muna matukar godiya ga ubangiji da ya tsirar da rayuwarmu daga wannan hatsarin jirgi. Dukkanmu muna cikin koshin lafiya kuma babu wanda wani abu ya same shi”

Leave A Reply

Your email address will not be published.